Wilshere zai iya barin Arsenal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jack Wilshere ba ya cikin sunayen wadanda za su taka wa Ingila wasa a Euro 2017

A shirye Arsenal yake da ya bayar da aron dan wasan kulob din na tsakiya, Jack Wilshere da wani babban kulob.

Dan wasan, shekara 24 wanda yake yawan samun rauni, ya buga leda sau uku ne kawai ga Arsenal, a kakar wasannin da ta gabata sakamakon raunin da ya samu a kwaurinsa.

Wilshere dai ya buga wa Ingila wasanni guda shida a lokacin bazara, duka suka hada da wasanni uku a gasar Euro 2016.

Sai dai kuma sunan Wilshere bai fito ba a jerin sunayen 'yan wasan da Sam Allardyce ya fitar a wannan makon.

Kulob din Arsenal dai ya sayi dan wasan tsakiya, dan kasar Switzerland,Granit Xhaka a kan £35m.

Labarai masu alaka