Chelsea ta sayi Marcos Alonso

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Karo na uku kenan Marcos Alonso zai taka-leda a gasar Premier

Kungiyar Chelsea ta sayi Marcos Alonso daga Fiorentina kan kudi fan miliyan 20.

Dan kwallon mai shekara 25, wannan ne karo na uku da zai buga gasar Premier.

Alonso ya buga tamaula a Bolton a shekarar 2010 zuwa 2013 daga nan ya koma Fiorentina, ita kuma ta bayar da shi aro ga Sunderland a bara.

Chelsea tana yin amfani Cesar Azpilicueta a matsayin mai tsaron baya daga barin hagu, hakan ya sa ta bayar da Baba Rahman aro ga Schalke.

Labarai masu alaka