Stoke City ta dauki Wilfred Bony aro

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wilfred Bony dan wasan Manchester City

Stoke City ta dauki Wilfred Bony, daga Manchester City, domin ya buga mata tamaula aro.

Bony dan kasar Ivory Coast ya buga wa City kwallaye 15 tun komawarsa Ettihad daga Swansea kan fan miliyan 28 a Janairun 2015.

Dan wasan mai shekara 27 bai buga wa City kwallo ba karkashin jagorancin Pep Guardiola.

Stoke ta kuma dauki golan Lee Grant domin ya buga mata wasanni aro zuwa watan Janairu.

Labarai masu alaka