An kusa fitar da rahoton gidauniyar Drogba

Image caption Didier Drogba yana buga tamaula a gasar Amurka

An kusa kammala hada wani rahoto a kan aikata ba daidai ba a yadda ake gudanar da Gidauniyar Didier Drogba, wadda ke tallafa wa masu karamin karfi.

A cikin watan Afrilu jaridar Daily Mail ta wallafa cewar fam dubu 14,111 aka kashe daga sama da fam miliyan daya da aka tara wa gidauniyar domin yin aikin agaji a nahiyar Afirka.

Hukumar da ke kula da cibiyoyin bayar da agaji ce ta kafa kwamitin bincike domin fayyace gaskiya, ta kuma ce kwamitin ya kusa kammala aikin da aka ba shi.

Drogba, tsohon dan kwallon Chelsea, ya ce rahoton babu gaskiya a cikinsa kuma an yi ne domin a bata masa suna.

A baya can ya fitar da sanarwa cewa babu batun cin hanci da zamba da almubazzaranci a gidauniyar tasa, rahotannin ba na gaskiya bane.

Labarai masu alaka