FA ta dakatar da Sergio Aguero

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasanni uku za a dakatar da Sergio Aguero

Hukumar Kwallon Kafar Ingila ta dakatar da dan wasan Manchester City, Sergio Aguero daga buga wasanni har guda uku.

Shi dai Aguero ya yi wa dan wasan West Ham, Wiston Reid gula, a karawar da suka yi a gasar Premier, a inda ka tashi 3-1, ranar Lahadi.

Alkalin wasan Andre Marriner bai ga laifin da Aguero ya yi ba a lokacin karawar.

Amma kuma daga bisani wani kwamitin alkalan wasa masu zaman kansu suka kalli fafatawar a talabijin suka kuma same shi da laifi.

Hukumar ta tuhumi Aguero da laifin rashin da'a.

Yanzu haka, Sergio ba zai buga karawa uku da kungiyar za ta yi ba ciki har da wasan hamayya da za ta fafata da Manchester United a ranar 10 ga watan Satumba.

Sergio Aguero dai ya ci wa Man City kwallaye uku a wasan da suka yi da Steaua Bucharest, a wasan gasar Champion League da suka tashi 5-0.

Labarai masu alaka