Guardiola ya so na zauna a City — Nasri

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Nasri zai buga wasanni aro a Sevilla

Samir Nasri ya ce kociyan Manchester City, Pep Guardiola, ya nemi da ya ci gaba da taka leda a kungiyar.

Nasri wanda ya koma Seville da murza-leda aro yana daga cikin 'yan wasa hudu da suka bar City zuwa wasu kungiyoyin domin taka-leda aron.

Pep Gaurdiola ya fadawa Nasri cewar ya kara teba a lokacin da kungiyar ke yin wasannin tunkarar kakar bana.

Nasri ya buga wasan da City ta doke West Ham 3-1 daga cikin wasannin hudu da kungiyar ta kara a bana.

Labarai masu alaka