An kara samun 'yan wasan Rasha da laifi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nadezhda Evstyukhina ta ci tagulla a gasar 2008

Kwamitin Olympic na duniya ya karbe lambar yabo daga wajen wasu 'yan wasan Rasha da aka samu da laifin amfani da abubuwa masu kara kuzari a gasar da aka yi a Beijing a 2008.

Kwamintin ya ci tarar 'yar wasan daga nauyi Marina Shainova wadda ta lashe azurfa da tagulla da kuma Nadezhda Evstyukhina da kuma 'yar tseren mita 400 ta 'yan wasa hudu Tatyana Firova.

Tun a baya kwamitin ya kwace lambar azurfa da Rasha ta lashe a tseren mita 400 ta 'yan wasan hudu da ta ci gasar da aka yi a 2008.

Kwamitin ya kuma ce ya hukunta wasu 'yan wasa biyar da aka samu da laifi, bayan da aka sake gwada tsohon samfurin da suka bayar.

'Yan wasan biyar dai sune:
  1. Tigran Martirosyan, dan Armenia. Mai daga nauyi ajin kilo 69 ya ci tagulla
  2. Alexandru Dudoglo, dan Moldova. Mai daga nauyi ajin kilo 69
  3. Intigam Zairov, dan Azarbaijan. Mai daga nauyi ajin kilo 85
  4. Yarelys Barrrios, 'yar Cuba. Mai wasan fai-fai
  5. Samuel Adelebari Francis, dan Qatar. Mai tseren mita 100

Labarai masu alaka