Ana binciken Franz Beckenbauer

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jamus ce ta karbi bakuncin gasar kofin duniya a 2006

Masu shigar da kara a Switzerland sun fara binciken Franz Beckenbauer da wadansu mutane uku bisa zargin cin hanci a gasar kofin duniya da Jamus ta karbi bakuncinta a 2006.

Ana zargin Beckenbauer, wanda mamba ne a kwamitin shirya gasar, da zamba da almubazzaranci da halalta kudin haram.

An kuma yi zargin aikata wannan laifin ne a yankin Switzerland.

Mista Beckenbauer, wanda ya jagoranci karbar bakuncin gasar kofin duniya a lokacin, ya karyata aikata ba dai-dai ba.

Labarai masu alaka