Bastian ba zai buga Europa League ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A baya dai Jose Mourinho ya ce Bastian ba zai kara buga wasa ba.

Sunan dan wasan tsakiya na Manchester United, Bastian Schweinsteiger, ba ya cikin jerin 'yan wasa 27 da za su taka wa kulob din leda a gasar Europa League ta bana .

Kocin Man United, Jose Mourinho ya fada wa dan wasan, mai shekara 23, dan kasar Jamus cewa ba zai kara taka leda ba, a kulob din.

Amma kuma ranar Juma'a, sunan dan wasan ya fito a jerin 'yan wasa 25 da za su yi wasannin gasar Premier.

A makon da ya gabata ne dai Bastian ya yi murabus daga buga wasannin kwallo na duniya.

Labarai masu alaka