Toure ba zai buga gasar Champions League ba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Watakila Yaya Toure ya koma Inter Milan

Kociyan Manchester City, Pep Guardiola bai sanya sunan dan wasan kulob din ba, Yaya Toure, a cikin jerin sunayen 'yan wasan da za su takawa kulob din leda, a gasar Champions League ta bana.

Daman dai sau daya ne Toure ya buga wasa a kakar nan a wasan da suka yi Stowa Bukarist wanda aka tashi 5-0.

Tuni ake ganin dangantaka ta yi tsami tsakanin Pep Guardiola da dan wasan dan kasar Ivory Coast, Yaya Toure.

Ana rade-radin Toure zai iya barin kulob din kuma ana cewa yana sansana Inter Milan.

Labarai masu alaka