Man City ta ƙalubalanci hukunta Aguero

Hakkin mallakar hoto Getty

Manchester City na kalubalantar tuhumar da hukumar kwallon kafar Ingila, FA take yi wa Sergio Aguero kan gular da ya yi wa dan wasan West Ham, Winston Reid.

Aguero, mai shekara 28, ya yi taho-mu-gama da Reid a wasan da suka yi ranar Lahadi, a inda suka tashi 3-1.

Idan har dai aka samu Aguero da laifi, to za a dakatar da dan wasan ne daga buga wasanni uku.

Daya daga cikin wasannin da dan wasan zai rasa sun hada da wanda Man City za ta fafata da Man United ranar 10 ga Satumba.

Labarai masu alaka