Messi ya ci wa Argentina kwallo

Lionel Messi ya sauya aniyarsa a watan Yuni

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Lionel Messi ya sauya aniyarsa a watan Yuni

Dan wasan Barcelona wanda dan kasar Argentina ne, ya sake ci wa kasar tasa kwallo, bayan da ya yi kome daga matsayinsa na farko na yin ritaya daga kwallon kasar.

Ya jefa kwallo daya a wasan da Argentina ta ci Uruguay 1-0, a wasannin neman cancantar shiga gasar Kudancin Amurka ta South America.

A watan Yuni ne dai Messi ya kudiri niyyar yin ritaya daga buga wa kasar wasa amma kuma bayan watanni biyu sai ya sauya tinani.

Argentina ce a gaba a gasar, a inda Brazil ke biye mata da maki biyu kacal.