Uganda ta samu shiga gasar kofin Afirka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A cikin watan Janairu za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka

Uganda ta samu tikikin buga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za ayi a badi, wanda rabon ta da shiga wasannin tun a shekarar 1978.

Uganda ta samu wannan matakin ne bayan da ta ci Comoros daya mai ban haushi a ranar Lahadi, inda ta kammala a mataki na biyu a rukuni na hudu da maki 13, Burkina Faso ce ta jagoranci rukunin.

Tunisia da Jamhuriyar Congo su ma sun samu tikitin, bayan da suka jagoranci rukunansu, inda Togo ce kasa ta biyu da aka yi wa alfarma bayan Uganda.

Kasashen da tuni suka samu shiga gasar tun kafin ranar Lahadi sun hada da Algeria da Kamaru da Masar da Ghana da Guinea-Bissau da Ivory Coast da Mali da Morocco da Senegal da kuma Zimbabwe.

Kasashe 16 ne za su kece raini har da mai masaukin baki Gabon a gasar kofin nahiyar Afirka da za a fara ranar 14 ga watan Janairu zuwa 5 ga watan Fabrairun 2017.

Labarai masu alaka