Shagon Shamsu ya buge Matawallen Kwarkwada

Image caption A turmi na biyu Shagon Shamsu ya buge Matawallen Kwarkwada

Abba Shagon Samsu kanin Emi ya buge Matawallen Kwarkwada a damben da suka yi a safiyar Lahadi a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a abuja, Nigeria.

Tun farko sai da Shagon Shamsu daga Arewa ya taka da Dogon Ministan daga Kudu tsawon turmi uku suka yi babu kisa alkalin wasa Tirabula ya raba su.

Nan da nan Matawallen Kwarkwada daga Kudu ya bukaci ya saka zare da Shagon Shamsu, a turmin farko da suka yi babu kisa.

Suna shiga turmi na biyu ne Shagon Shamsu ya buge Matawallen Kwarkwada, sai da aka dauki lokaci kafin matawallen ya dawo hayyacinsa.

Sauran wasannin da aka yi Nuran Dogon Sani daga Arewa da Kurarin Kwarkwada daga Kudu ta shi suka yi Canjaras.

Garkuwan Sojan Kyallu daga Arewa buge Shagon Indali daga Kudu ya yi a turmin farko, Shi ma Shagon Bababangida Kyade daga Arewa doke Fatalwar Shagon Alabo daga Kudu ya yi a turmin farko.

Labarai masu alaka