Allardyce ya fara jan ragamar Ingila da nasara

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ingila ta doke Slovakia da ci 1-0 har gida

Sam Allardyce ya fara jagorantar tawagar kwallon kafa ta Ingila da kafar dama, bayan da ya ci Slovakia 1-0 a wasan neman shiga gasar kofin duniya da suka kara a ranar Lahadi.

Adam Lallana ne ya ci wa Ingila kwallon daf da za a tashi daga karawar, kuma Slovakia ta karasa fafatawar da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Martin Skrtel jan kati.

Da wannan nasarar da Allardyce ya samu ya zama mai horarwa na tara da ya ci wasan farko da ya fara jan ragamar tawagar Ingila a tarihi.

Ga sakamakon wasu wasannin da aka yi:
  • Jamhuriyar Czech 0 Ireland ta Arewa 0
  • Malta 1 Scotland 5
  • San Marino 0 Azerbaijan 1
  • Denmark 1 Armenia 0
  • Kazakhstan 2 Poland 2
  • Lithuania 2 Slovenia 2
  • Norway 0 Jamus 3
  • Romania 1 Montenegro 1

Labarai masu alaka