Ivory Coast ta samu tikitin buga kofin Afirka

Image caption Ivory Coast ce mai rike da kofin nahiyar Afirka da ta lashe a 2013

Mai rike da kofin Nahiyar Afirka, Ivory Coast, ta samu gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a shekarar 2017 a Gabon.

Ivory Coast ta samu kai wa wasannin da za a yi a badi ne, bayan da ta tashi kunnen doki 1-1 da Saliyo a ranar Asabar.

Ivory Coast ce ta fara cin kwallo ta hannun Jonathan Kodjia saura minti takwas a je hutun rabin lokaci, bayan da aka dawo ne Saliyo ta farke ta hannun Al-Hadji Kamara.

Senegal ma ta samu kai wa gasar da za a fara a cikin watan Janairu, bayan da ta doke Namibia da ci 2-0, kuma ita ce kasar da ta lashe dukkannin wasanni shida da ta yi.

Nigeria ta doke Tanzaniya da ci daya mai ban haushi a ranar Asabar, kasashen biyu ba su sami tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar ta Afirka ba da za ayi a badi.

Labarai masu alaka