Messi ba zai buga karawa da Venezuela ba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Messi ya koma buga wa Argentina tamaula, bayan da ya ce ya yi ritaya a baya

Lionel Messi ba zai buga wa Argentina wasan neman shiga gasar kofin duniya da za ta yi da Venezuela a ranar Talata, sakamakon raunin da ya yi.

Dan kwallon wanda ya koma yi wa tawagar kasar tamaula, bayan da ya sanar da yin ritya, ya yi rauni ne a fafatawar da Argentina ta ci Uruguay daya mai ban haushi a ranar Alhamis.

Messi ne ya ci kwallon da ya bai wa Argentina damar kai wa mataki na daya a kan teburi a rukunin wasannin Kudancin Amurka.

Bayan da rukunin Kudancin Amurkan ya yi wasanni bakwai daga 18 da zai yi, Argentina ce ta daya sai Uruguay sai Colombia sannan Ecuador, Brazil tana mataki na biyar.

Kasashe hudu ne za su samu gurbin buga gasar kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018 daga Kudancin Amurka kai tsaye, yayin da kasa ta biyar ta buga wasan cike gurbi.

Labarai masu alaka