El-Kanemi ta ci Tornadoes 2-0

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Sakamakon wasan mako na 34 a gasar Firimiyar Nigeria

El-Kanemi Warriors ta doke Niger Tornadoes da ci 2-0 a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na 34 da suka kara a ranar Lahadi.

Kano Pillars ma 2-0 ta ci Sunshine Stars ta Akure a Kano, Lobi Stars kuwa daya mai ban haushi ta ci Enyimba International.

Rangers kwallaye 4-0 ta zazzagawa Rivers United, yayin da Ikorodu United ta ci Heartland 1-0 har gida.

Ita ma Plateau United daya mai ban haushi ta ci Shooting Stars, Akwa United kuwa 3-1 ta doke MFM.

Ga sakamako wasannin da aka yi:
  • Heartland 0 vs Ikorodu United 1
  • Kano Pillars 2 vs Sunshine Stars 0
  • Plateau United 1 vs Shooting Stars 0
  • Rangers 4 vs Rivers United 0
  • Warri Wolves 1 vs Nasarawa United 0
  • Akwa United 3 vs MFM 1
  • Lobi Stars 1 vs Enyima 0

Labarai masu alaka