An fitar da Konta a gasar tennis ta US Open

Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Johanna Konta ita ce ke mataki na daya a iya kwallon tennis a Birtaniya

Johanna Konta ta yi ban kwana da gasar kwallon tennis ta US Open, bayan da Anastasija Sevastova ta doke ta a ranar Lahadi.

Konta ta yi rashin nasara ne da ci 6-4 da kuma 7-5 a hannun Sevastova wadda ta yi ritaya daga wasan a shekarar 2013, amma ta sake dawowa ruwa.

Sevastova 'yar kasar Latvia za ta kara da Caroline Wozniacki ta Denmark a wasan daf da na kusa da karshe.

Labarai masu alaka