An ci kwallo 643 a gasar Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto npfl Twitter
Image caption An kammala wasannin mako na 34 a gasar Firimiyar Nigeria

Kwallaye 643 aka ci a gasar Firimiyar Nigeria, bayan da aka buga wasanni 306.

Daka cikin wannan adadi, kungiyoyin da suka je wasanni a waje ne suka ci kwallaye 160.

A ranar Lahadi aka buga wasannin mako na 34, an kuma zura kwallaye 16 a raga. Rangers ce ta fi cin kwallaye a makon, inda ta ci Rivers United 4-0.

Rangers tana mataki na daya a kan teburi da maki 54 sai Rivers United da maki 53, yayin da Wikki Tourist mai kwantan wasa daya tana matsayi na uku da maki 51.

Labarai masu alaka