'Wariyar launin fata na karuwa a harkar kwallo'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan wasa a lokacin gasar Euro 2016

Kungiya mai fafutukar kawo karshenwariyar launin fata a harkar wasanni ta ce ana samun karuwar nuna kiyayya tsakanin 'yan wasan kwallo a kowane mako.

Kungiyar ta ce ta karbi korafe-korafe 402 a kakar wasannin da ta gabata.

Hakan na nuni da cewa an samu karuwar kiyayyar idan aka yi la'akari da koke 393 da kungiyar ta karba a kakar wasa ta 2014-15.

An ce an sami karuwar kalaman batanci ga 'yan wasa ta shafukan sada-zumunta, guda 194.

Wannan dai na zuwa bayan da wasu alkaluma suka nuna cewa an sami karin kaso 20 na karuwar ayyukan kin jinin juna a Burtaniya da Wales.

Kungiyar dai na neman masu tallafa wa da shugabannin kwallon kafa da su yi aiki tare wajen kawo karshen nuna kiyayya.

Labarai masu alaka