Eriksen zai cigaba da zama a Tottenham

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Christian Eriksen ya zuba wa Tottenham kwallaye takwas a kkar wasannin da ta gabata

Dan wasan Tottenham na tsakiya, Christian Eriksen ya rattaba hannu kan sabon kwantaragin da kulob din na tsawon shekara hudu.

Dan wasan, dan kasar Denmark, mai shekara 24 ya buga wasanni 134 ga Tottenham tun da ya fara taka leda da kulob din a watan Agustan 2013, bayan da ya baro Ajax.

Eriksen ya ci kwallaye takwas a kakar wasannin da ta gabata.

A shafinsa na intanet, dan wasan ya wallafa cewa "ina kallon akwai nasara a kulob din nan kuma ba zan rattaba hannu ba idan da a ce ban ga nasarar ba."

Labarai masu alaka