Nicklas Bendtner zai koma Forest

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Nicklas Bendtner a lokacin yana taka wa Arsenal leda

Kungiyar wasa ta Nottingham Forest na kokarin sayen tsohon dan wasan Arsenal, Nicklas Bendtner.

Dan wasan na gaba, mai shekara 28 wanda dan kasar Denmark ne ya bar Wolfsburg a farkon wannan shekarar bayan da kwantaraginsa ya kare.

Bendtner dai ya zura wa Arsenal kwallaye 45 a wasanni 171 tsakanin 2005 zuwa 2014.

Arsenal ta bayar da aron dan wasan ga Sunderland da Birmingham da Juventus.

Bendtner ya ci wa kasarsa kwallaye 29 a wasanni 72.

Labarai masu alaka