Ko ka san yawan kociyoyin da Palermo ta yi?

Image caption 'yan wasan Polermo na murna

Kungiyar wasa ta Palermo ta nada Roberto de Zerbi a matsayin sabon koci, bayan da Davide Ballardini ya yi murabus ana dab da fara gasar Serie A ta wannan kakar.

De Zerbi, mai shekara 37, ya horas da Foggia a baya, kafin ya bari ya koma wani kulob mai matsayi na uku a gasar ta Seria A.

A kakar wasannin da ta gabata kadai, sai da shugaban Palermo, Maurizio Zamparini ya nada kociyoyi takwas.

A watan Janairu 2016 ne dai aka kori Ballardini daga horas da kulob in na Palermo, kafin daga bisani a sake mayar da shi a watan Afrilu.

A lokacin ne kuma ya taimaka wajen hana kulob din fadowa daga teburin gasar Seria A.

Yanzu haka, Palerrmo ce ta 15 a teburin gasar ta Serie A, a inda take gaba da Inter Milan da maki daya kacal.

Zamparini wanda ya sayi Palermo a 2012, ya nada kociyoyi kusan 60 a tsawon shekaru 29 da ya kwashe a matsayinsa na mamallakin kulob.

Labarai masu alaka