Tennis: Serena ta samu nasara ta 308

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Serena Williams ta dara Roger Federer a yawan cin wasanni

'Yar wasan tennis mai matsayi na daya, Serena Williams ta samu nasara kan abokan wasanta karo na 308, bayan da ta doke 'yar wasan Kazakhstan, Yaroslava Shvedova, a gasar US Open.

'Yar wasan, mai shekara 34 wadda 'yar Amurka ce ta samu nasarar cin wasan nata ne da ci 6-2 da 6-3.

Wannan ne kuma ya sa ta dara dan wasan na Tennis, Roger Federer a daukacin manyan wasannin da ya samu nasara.

Yanzu haka, Serena za ta fafata da dan kasar Romania, Simona Halep, a wasan kusa-da-karshe.

Serena Williams ta ce " ta samu nasara da yawa."

Ta kara da cewa "gaskiya babban abin murna ne. Ban zaci zan cigaba da wasa ba har kawo yanzu. Kuma ba na tunanin zan daina wasa."

Labarai masu alaka