Tennis: Murray ya cancanci wasan dab-da-karshe

Hakkin mallakar hoto ALLSPORT
Image caption Andy Murray yana murnar samun nasara

Dan wasan Tennis na Burtaniya, Andy Murray ya cancanci zuwa wasan dab-da-na-kusa-da-karshe, bayan da ya buge dan wasan Bulgaria, Grigor Dimitrov, a gasar Tennis ta US Open.

Murray, mai matsayi na biyu a gasar, ya buge Grigor Dimitrov da ci 6-1 da 6-2 da 6-2.

Yanzu haka dai Andy Murray zai fafata da Kei Nishikori a wasan dab-da-na-kusa-da-karshe.

A wasan mutum bibiyu kuma, Jamie Murray da Bruno Soares sun samu gurbin shiga wasan dab-da-na-kusa-da-karshe bayan da suka buge Brian Baker da Marcus Daniell.

Labarai masu alaka