Ingila ta goyi bayan van Praag ya shugabanci Uefa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a yi zaben shugaban hukumar kwallon kafa na Turai a ranar 14 ga watan Satumba

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ce za ta mara wa shugaban hukumar kwallon kafar Netherland, Michael van Praag, baya, domin ya shugabanci hukumar kwallon kafa ta Turai.

Van Praag mai shekara 68, mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai, zai yi takara da Aleksander Ceferin na Slovenia a zaben da za a yi a ranar 14 ga watan Satumba.

Hukumar na neman wanda zai jagorance ta bayan da Michel Platini ya yi murabus bisa kasa cin nasara a karar da ya shigar kan dakatar da shi da aka yi daga shiga sabgogin tamaula.

An samu Platini da laifin karya dokar da'ar ma'aikata ta hukumar Fifa, bayan da aka biya shi ladan aiki na kudi sama da fam miliyan daya da Sepp Blatter ya yi masa.

Labarai masu alaka