Enyimba ta doke Wikki Tourist da ci 2-1

Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption Rangers ce ke mataki na daya a kan teburin Firimiyar Nigeria

Enyimba International ta samu nasara a kan Wikki Tourist da ci 2-1 a kwantan wasan gasar Firimiya Nigeria da suka fafata a ranar Laraba.

Wikki ce ta fara cin kwallo ta hannun Godwin Obaje saura minti uku a je hutun rabin lokaci, kuma daf da za a je hutun Nzube Anaezemba ya farkewa Enyimba.

Bayan da aka dawo ne daga hutun Nzube Anaezemba ya kara ta biyu a ragar Wikki, inda hakan ya bai wa Enyimba damar hada maki uku a karawar.

Daya kwantan wasan da aka yi tsakanin Abia Warriors da FC Ifeanyiubah tashi suka yi canjaras 1-1.

Labarai masu alaka