Nottingham Forest ta dauki Nicklas Bendtner.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bendtner tsohon dan kwallon kungiyar Arsenal

Kungiyar Nottingham Forest ta sanar da cewar ta dauki tsohon dan wasan Arsenal, Nicklas Bendtner.

Dan wasan mai shekara 28, wanda dan kasar Denmark ne ya bar Wolfsburg a farkon wannan shekarar bayan da kwantaraginsa ya kare.

Bendtner dai ya zura wa Arsenal kwallaye 45 a wasanni 171 tsakanin 2005 zuwa 2014.

Arsenal ta bayar da aron dan wasan ga Sunderland da Birmingham da Juventus.

Labarai masu alaka